Download PDF
Back to stories list

Andiswa Kwararriyar ‘yarwasan Kwallan Kafa Andiswa Soccer Star

Written by Eden Daniels

Illustrated by Eden Daniels

Translated by Muhammad Umar

Language Hausa

Level Level 2

Narrate full story The audio for this story is currently not available.


Andiswa ta na kallan yara maza suna wasan kwallan kafa. Ta so a ce ta na cikin su. Ta tambayi Maiharar da ‘yanwasan ko za ta iya shiga cikinsu ta yi wasa.

Andiswa watched the boys play soccer. She wished that she could join them. She asked the coach if she can practise with them.


Maihorar da ‘yanwasa ya dora hannuwansa akan kugunsa yace “A wannan makaranta maza ne kadai aka bari su yi wasan kwallan kafa.

The coach put his hands on his hips. “At this school, only boys are allowed to play soccer,” he said.


‘Yanmaza suka ce mata ta ta tafi ta yi wasan kwallan da ake da hannu, ita ce ta mata, kwallan kafa ta maza ce. Andiswa ta damu.

The boys told her to go play netball. They said that netball is for girls and soccer is for boys. Andiswa was upset.


Kashe-gari, makarantar za ta yi babban wasa. Maihorar da ‘yanwasa ya damu saboda kwararran Danwasan sa ba yi da lafiya kuma ba zai iya wasa ba.

The next day, the school had a big soccer match. The coach was worried because his best player was sick and could not play.


Andiswa ta ruga wajan Maihorar da ‘yanwasa ta roke shi ya kyale ta, ta yi wasa. Maihorar da ‘yanwasa ya rasa yadda zai yi. Sai ya yanke shawra Andiswa ta shiga cikin su.

Andiswa ran to the coach and begged him to let her to play. The coach was not sure what to do. Then he decided that Andiswa could join the team.


Wasa ya yi zafi, ba wanda ya ci kwallo a farkon rabin lokaci.

The game was tough. Nobody had scored a goal by half time.


Lokacin da aka juya rabin lokaci na biyu, sai wani daga cikin su ya turawa Andiswa kwallo. Sai ta ruga da sauri kusa da wallo (goal). Andiswa tadoki kwallo da karfi ta ci

During the second half of the match one of the boys passed the ball to Andiswa. She moved very fast towards the goal post. She kicked the ball hard and scored a goal.


‘Yankallo suka mike da murna. Tun daga ranar aka kyale mata suna yin wasan kwallan kafa a wannan makaranta.

The crowd went wild with joy. Since that day, girls were also allowed to play soccer at the school.


Written by: Eden Daniels
Illustrated by: Eden Daniels
Translated by: Muhammad Umar
Language: Hausa
Level: Level 2
Source: Andiswa Soccer Star from African Storybook
Creative Commons License
This work is licensed under a Creative Commons Attribution-NonCommercial 3.0 International License.
Read more level 2 stories:
Options
Back to stories list Download PDF