Duk da kwazan da ta ke da shi, iyayanta ba sa san ta je makaranta domin taimaka masu aiki a gida. Da ta cika shekara bakwai sai yayanta ya rinjayi iyayenta domin ta je makaranta.
A Jami’ar Amuruka ta koyi sababin abubuwa da yawa, wadanda suka hada da rayuwar tsirai da yadda suke girma da yadda suke wasa da ‘yan uwanta a karkashin inuwar kyakkyawan bishiyoyin Kenya a daji.
Da zarar ta koyi wani abu ya kan kara mata kaunar mutan Kenya, ta na son ganin su cikin farin ciki da ‘yanci, ta kan kuma tuna Afurika a matsayin gida.
Yayin da kamala karatun ta, sai ta dawo gida. Amma kasarta ta canja, manyan gonaki sun hade hade da hanya. Mata basu da itacen girki sanan jama’ar gari sun talauce, yara suna fama da yunwa.
Wangari ta taimakawa mata sosai sun sami kudi saboda ta koya musu yadda za su shuka bishiyoyi su sayar dan taimakawa iyalensu. Wannan yasa mata suka zama masu alfahari da kansu.
Bayan lokaci mai tsawo bishiyoyi sun girma sun zama daji, koguna suka fara gudanya, sakonta sai ya fara mamaye Afurika. A yau milliyoyin bishiyoyi sun samu a sakamakon gudunmuwar irin da Wangari ta samar.
Mutanen duniya baki daya sun yaba da kwazon ta, saboda haka ne ma aka karama ta da shahararriyar kyautar nan ta zaman lafiya ta duniya (NOVEL). Ita ce mace ta farko da ta fara samun kyautar a Afurika.
旺加里努力工作,引起了全世界的注意,人们授予她诺贝尔和平奖,她是非洲第一位获得这份殊荣的女性。
Wangari ta mutu a shekara ta dubu biyu da sha daya (2011), amma mu kan tuna ta duk lokacin da muka ga kyawawan bishiyoyi.