Garkar kaka tana ban shawa, akwai
dawa, da hatsi kuma da rogo.
Amma ma fi mahimmanci shine
ayaba.
Koda yake kaka tana da jikoki da
yawa, na sani da ni ta fi ƙwauna.
Tana gayyata ta a gidanta. Tana
gaya mini abubuwa da dama.
Amma akwai abin ba ta gaya mini:
Wurin da take nana ayaba.
Wata rana, na ga wani babban
kwando na haki ajiye cikin rana a
gaban gidan kaka.
Da na tambaye ta, mine ne amfanin
Kwandon,sai ta ba ni amsa kamar
haka: “Kwandon mamaki ne”. A
kusan kwandon, akwai ganyen
ayaba da kaka take jujjuyawa lokaci
suwa lokaci.
Na yi mamaki. “Mine ne amfanin
wannan ganyen kaka?” na tambaye
ta. Sai ta ba ni amsa kamar haka:
”Ganyen mamaki ne”.
Akwai shawa in kana kallon kaka,
ayaba, ganyen ayaba da kuma
babban kwandon na haki. Amma
kaka ta sanya ni in kiranyo
ma’aifiyata don nemo wani abu.
“Kaka,don Allah, bar ni in ga abin da
kike gyarawa…”
“Kar ki zama maras ji, jikata, ki yi
abin aka ce ki yi” kaka take faɗi. Sai
ni kuma in tafi da gudu.
Bayan na komo, kaka tana zamne
waje, amma ba kwando, ba ayaba.
“Kaka, ina kwando, ina dukkan
ayabar, kuma ina…”
Sai ta ba ni amsa kamar haka:
“Suna wani wuri na mamaki”. Ban ji
daɗi ba.
Bayan kwana biyu, kaka ta aike ni
cikin ɗakinta in ɗauko wata sanda
da take tokarawa ta yi tafiya.
Ko da na buɗe ƙofar sai ƙamshi
nunannan ayaba ta tarbo ni. Tsakar
ɗakin, akwai babban Kwandon
mamaki na kaka. An ɓoye shi cikin
wani babban bargo. Na ɗaka shi na
ji wannan ƙamshi mai daɗi.
Sai na ji muryar kaka, na zabura,
“Mi kike yi? Ki yi maza ki kawo mini
sandar”.
Ni kuma na yi maza na ɗauko
sandar.
“Mi kike ma murmushi?” in ji kaka.
Tambayar tata, ta sanya na gano da
cewa, murmushina na gano wuri
mamakin da kaka take faɗi.
Washe–gari, lokacin da kaka ta zo ta
ga ma’aifiyata, ni kuma sai na ruga
gidanta don in ƙara ganin ayabar.
Akwai da yawa da suka nina. Na
ɗauki ɗaya na ɓoye cikin rigata.
Bayan na gano kwando, sai na laɓe
bayan ɗaki na canye da sauri. Ban
taɓa cin ayaba mai daɗin wannan
ayabar.
Washe–gari, lokacin da kaka take
cikin garkar tana tattara kayan
garka, na sake komawa cikin ɗakin
nata don in ga ayabar. Sun fara
nina.
Ban yi hanƙuri ba kuma na ɗauko
hudu. Ina fitowa sannu sannu sai na
ji kaka ta yi wani ɗan tari waje. Na
ɓoye ayabar cikin riga, kaka kuma
ya wuce.
Washe-gari, ranar kasuwa ce. Kaka
ta tashi tun da safe.
Kullum tana kai ayaba da rogo don
ta saida a kasuwa.
Ranan nan, ban je ba na gaida
kaka. Amma zan je in iske ta.
Can da maraice, babana da kaka
sun kiranyo ni. Ni san abin da na yi.
Daren nan, da na kwanta, na yi
tunanin da ba ni ƙara satar kakata
ko ma’aifina ko wani can daban.