Wata rana da farar safiya, kakar Idi
ta yi kiran shi, “Idi, don Allah, kana
iya kai ma mahaifanka wannan
ƙwan? Suna son su yi wani babban
biskiti na auren ƙanwarka”.
Lokacin da yake zuwa gida
mahaifan nashi, Idi ya gamu da
wasu samari biyu suna cirar ƴaƴan
itace. Ɗaya daga cikin yaran ya
ɗauki ƙwai ɗaya kuma ya jefa
saman iccen. Ƙwan ya fashe.
福思带着鸡蛋上了路,他遇到了两个正在采水果的男孩。其中一个男孩抓过鸡蛋,朝着果树扔过去,鸡蛋破了。
“Mi ka yi?” in ji Idi. “Wannan ƙwan
na yin biskiti ne, biskitin auren
ƙanwata. Mi ƙanwar tawa za ta ce
idan babu biskitin aurenta?”
Samari ba su ji daɗin wannan
wasan da suka yi ma Idi.
“Babu yadda zamu yi don yin
biskiti, amma ga wannan sandar ka
kai ma ƙanwarka.” In ji ɗaya daga
cikin su. Idi ya ci gaba bisan
hanyarshi.
Bisan hanya, ya tarda mutane biyu
suna gina wani gida. “Muna iya
amfani da wannan sandar taka mai
ƙwari?” in ji ɗaya daga cikin
mutanen biyu. Amma da yake
sandar ba ta da ƙwari sosai, sai ta
kariye.
“Mi kuka yi?” in ji Idi.
“Wannan sandar kyauta ce aka ma
ƙanwata. Masu ciran ɗiyan itace
suka ba ni don sun fasa ƙwan da za
yi biskitin auren ƙanwata. Biskitin
na auren ƙanwata ne. Yanzu ba
ƙwan, ba biskitin kuma babu kyauta
ko ɗaya.”
Mi ƙanwar tawa za ta ce.
Maginan ba su ji daɗi ba da suka
karya sandar.
“Ba mu san abinda za mu yi ba,
amma ga ciyawa kaɗan ka kai ma
ƙanwarka,” in ji ɗaya daga cikinsu.
Idi ya ci gaba bisan hanyarshi.
Bisan hanya, Idi ya tarda wani
makiyayi da saniya.
“Wannan ciyawar sai ta yi daɗi, ko
ka ba ni kaɗan?” in ji saniyar.
Sai da yake ciyawar tana da daɗi,
saniyar ta cinye duka.
“Mi kika yi?” in ji Idi.
“Wannan ciyawar, kyauta ce aka ma
ƙanwata. Magina sun ba ni ciyawar
don su karya sandar cirar ɗiyan
itace. Masu cirar ɗiyan itace sun ba
ni sandar don sun fasa ƙwan yin
biskitin auren ƙanwar tawa. Biskitin
na auren ƙanwata ne. Yanzu babu
biskitin, ba kuma kyauta ko ɗaya.
Mi ƙanwar tawa za ta ce?”
Saniya ba ta ji daɗi ba da ta cinye
ciyawar. Makiyayin ya ɗauki niyyar
bada saniya don ta raka shi kuma ta
zama kyauta ga ƙwanwarshi. Idi ya
ci gaba bisan hanyarshi.
奶牛很抱歉,因为它太自私了。农民决定让奶牛跟着福思,作为礼物送给他姐姐。福思继续上路了。
Sai dai lokacin da za a yanka
saniyar, sai ta gudu ta koma ga mai
ita. Idi kuma ya ɓadda sawunta.
Ko da ya zo wajen auren ƙanwar
tashi, mutane sun yi abinci.
但是,到了吃晚饭的时候,奶牛跑回农场了,福思也迷路了。他很晚才到姐姐的婚礼上,客人们已经在吃饭了。
“Mi za ni yi ?” in ji Idi.
“Saniyar da ta gudu, kyauta ce
kambacin ciyawar da magina suka
ba ni. Magina sun ba ni ciyawar don
sun karya sandar cirar ɗiyan itace.
Masu cirar ɗiyan itace sun ba ni
sandar don sun fasa ƙwan yin
biskitin auren ƙanwar tawa. Biskitin
na auren ƙanwata ne.
Yanzu babu saniyar, ba biskitin, ba
kuma kyauta ko ɗaya.”
Ƙanwar ta Idi ta yi tunani kuma ta
ce: “Idi ƙanena, ban damu da
wannan kyautar. Ban damu da
biskitin ba. Yau ranar murna ce, ina
farin ciki. Sanya tufafinka na salla
ka zo mu raya wannan ranar!”
Sai idi ya yi hakan.