Kaza da shanshani abokai ne.
Amma kullum suna takara
tsakaninsu. Wata rana, sai suka yi
niyyar wasan ƙwallon ƙafa don
sanin wa ya fi kwaninta tsakani su
biyu.
鸡和千足虫是好朋友,但是它们又互相竞争。有一天,它们决定进行一场足球比赛,看看谁是最棒的球员。
Sai suka shiga filin ƙwallon ƙafar
kuma suka fara wasan. Kaza tana
da gaugawa amma shanshani ta fi
ta gaugawar. Kaza ta harba ƙwallon
nesa amma kuma shanshani tana
aika ƙwallon nesa ƙwarai fiye inda
na kazar zai je. Ganin haka, sai da
kaza ta fara hassala.
Ƴan takarar biyu sun yi niyyar
su je bugun da kai sai mai tsoron
gida. Da farko shanshani ita ce mai
tsaron gida wato gola kenan. Kaza
ta saka ƙwallo ɗaya rak cikin raga.
Sai aka juya, kaza ta zama ma gola
mai tsaron gida.
Shanshani ta harba ƙwallo, kuma ta
saka a raga. Shanshani tana
gwaninta kuma tana saka ƙwallon.
Shanshani ta saka ƙwallon har da
kai. Shanshani ta saka ƙwallon biyar.
Kaza ta hassala da rishin nasarar da
ta yi. Kaza ba ta iya wasa ba.
Shanshani ta yi ta dariya saboba
abokiyarta ta hassala wajen wasa.
鸡输了,它很生气。千足虫哈哈大笑,因为它的朋友输了球,就无理取闹。
Sai kaza ta buɗe babban bakinta ta
haɗiye shanshanin.
鸡生气极了,它张开嘴,一口把千足虫吞了下去。
Lokacin da kaza tana shigowa gida,
sai ta gamu da uwar shanshani. Sai
ta ce mata, “ba ki ga ɗiyata ba?”
Kaza ba ta amsa mata ba. Uwar
shanshani ta damu.
Sai uwar shanshani take ji wata
ƙaramar murya tana cewa: “Ki
agaje ni uwata!” Shanshani take
faɗi.
Uwar shanshani ta dubu kewayenta
da kyau. Muryar nan da cikin kaza
ta fito.